Labarai
Trending

Auren Murja Ibrahim Da Me Barandar Nono (Jaruman TikTok)

An dade ana yada labarin cewa Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya da takwaran ta shima Jarumin TikTok Ashiru Idris (Me Barandar Nono) zasu yi aure, kamar yanda wannan labari ya karade ko ina a shafukan yanar gizo (shafukan sada zumunta). Hakan yasa wannan kafa me Albarka ta Taskar Nasaba ta tafi bincike dan gano gaskiyar al’amari.

Me Baranda da Murja

GASKIYAR MAGANA

A binciken da muka yi mun gano yanda wani daga cikin mawakan masana’antar Kannywood wato mawaki Lilin Baba ya bayyana cewa; indai da gaske suke shi zai biya kudin sadakin auren nasu,l da akwatin lefe, kamar yadda ya bayyana a shafin Instagram yayin suke suke “live video” da jarumar a shafin Instagram din.

Sannan kuma binciken namu ya gano yanda Ashiru Idris (Me Barandar Nono) yake dora hotuna tareda video wanda suke tareda Murja a shafukan sa na Instagram da TikTok tareda fadin wasu kalamai na soyayya inda yake cewa; “Allah ne kaɗai yasan irin son da nakewa wannan baiwar Allah” Duba da wannan kalamai da kuma wannan hujjoji bincike ya nuna cewa; tabbas akwai maganar soyayya tsakanin Murja Ibrahim Kunya (Jarumar TikTok) da Ashiru Idris (Me Barandar Nono), kuma da alama soyayyar ta gaskiya ce duba da wannan abubuwa da suke faruwa.

ABIN LURA

Tabbas komai na iya faruwa ko aure ko akasin haka, duba da yanda Lilin Baba yayi wannan alkawari tabbas akwai maganar soyayya tsakanin su, ba abin mamaki bane idan aka ce sunyi aure, domin ba a kansu aka fara yin irin wannan ba, (Jaruma ta auri Jarumi ko Jarumi ya auri Jaruma). Saidai idan hakan ta kasance a kansu aka fara ganin Jarumin TikTok ya auri Jarumar TikTok.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button