
Yajin aikin ASUU ya ƙare, bayan wata kotu ta umarci kungiyar da ta koma bakin aiki ba tareda bata lokaci ba.
Hakan na faruwa ne bayan kungiyar ta daukaka kara saboda hukuncin da kotun gwadago tayi na cewa kungiyar malaman ta ASUU ta koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba, hukuncin da kungiyar bata aminta dashi ba, hakan ne yasa ta daukaka karar zuwa wannan kotun, inda ita ma ta yanke wannan hukuncin.

Kafin yanke hukuncin kotun ta shawarchi ASUU da Gwamnatin Nigeria suke su sasanta kansu a wajen kotu, saidai kuma abin yaci tura, kamar yadda Femi Falana (Lauyan ASUU) ya shaidawa kotun.
Shima James Igwe (Lauyan gwamnati) ya bayyanawa kotu cewa sasancin bazai yiwu ba.
Hakan yasa kotun ta yanke hukunci cewa; ASUU ta janye yajin aikin kuma a koma makaranta ba tareda bata lokaci ba.
ABIN LURA
Yanzu dai zamu iya cewa yajin aikin ASUU ya ƙare, duba da wannan hukuncin na kotun daukaka kara.