Labarai
Trending

An Kama Wani Babban Soja Na Siyarwa Yan Bindiga Makamai

Wani rahoto da muka samu na cin amanar ƙasa tareda aikin soja, wanda wani babban jami’in soja wanda ake zargi da laifin siyarwa tareda bada hayar bindigogi da harsasai ga yan ta’adda da yan kidnapin wadanda suka addabi kasar nan, anan ma dai jami’an Yan Sanda ne suka kama maci amanar tare da taimakon yan banga.

INDA AKA KAMASHI

Jami’in mai suna Nafiu ya kasance yana aiki a barikin sojojin Muhammadu Buhari dake tungan mage a Abuja, an kama shi ne a filin shakatawa na Dankogin Zuba a Abuja.

Wanda ake zargi

YANDA AKA KAMASHI

Yanda aka kama sojan mai mukamin kofur shine; an kama wasu masu karkuwa da mutane aka tambaye su ina suke samun makamai anan ne sunan wannan sojan ya fito, daga nan suka hada dabara, inda suka umarci yan kidnapin din da su nemi ya kawo muku bindiga kirar AK47 su siya domin yin wani sabon operation, ya dauko sabuwar bindiga a cikin motarsa da nufin ya siyar musu akan kuɗi Naira miliyan uku ba tareda ya fahimci tarko aka naɗa masa ba, zuwan sa keda wuya jami’an tsaron yan sanda suka chafke shi. Yanzu Nafiu yayi nadama mara amfani.

ABIN LURA

Dama al’umma nada shakku akan jami’an tsaron kasar nan, musamman sojoji. Domin ko kwanan nan ma an kama wasu jami’an sojan a garin Jajimaji dake jihar Yobe bisa zargin su da harbe wani malamin addinin Muslunci da nufin sace masa mota.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button